Ni Da El Rufa’i Mutu Ka Raba – Hadiza Bala Usman

Dakatacciyar shugaban Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Najeriya, Hadiza Bala ta bayyana cewa, ita da gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, takalmin kaza ne, Ogan ta ne na dindindin babu tantama akai.

Hadiza ta rubuta a shafinta ta Facebook a karkashin wani hotunta zaune da gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai a Zariya wajen hawan karamin Sallah a fadar mai martaba Sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli.

” Eid Mubarak….”Taqabbalallāhu minnā wa minkum.

Allah ya amsa ayyukan mu na kwarai. Ina fadar mai martaba sarkin Zazzau tare da shugabana na har abada @El-Rufai. Muna nan daram dam, domin akan gaskiya muka dogara a koda yaushe. Muna rokon Allah ya kare mu yayi mana jagora, Amin. ”

Idan ba a manta ba, kafin a nada Hadiza shugabar Hukumar NPA, ita ce shugabar ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Kaduna.

Labarai Makamanta

Leave a Reply