Sanata Abdulaziz Yari daga Zamfara ta Yamma ya karyata rahoton da ke yawo na cewa ya hada kai da Atiku Abubakar domin kafa sabuwar jam’iyyar siyasa.
Rahotannin sun ce ya hada kai da Abubakar, da kuma Sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya, Abdul Ningi da aka dakatar a halin yanzu don kafa jam’iyyar.
An ruwaito cewa Atiku yana so ya kafa sabuwar jam’iyyar a matsayin wani shiri na kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2027.S
Sai dai Atiku ya musanta wannan zargin, inda ya bayyana cewa ya mayar da hankali ne kawai wajen samar da hadin kai a tsakanin jam’iyyun adawa.
Tawagar Yari ta kafafen yada labarai ta sanar a ranar Laraba cewa tsohon gwamnan Zamfara fitaccen mutum ne a cikin jam’iyyar APC kuma yana tafiya ne kan manufofinta.
“Ofishin yada labarai na mai girma Sanata Abdulaziz Yari, ya musanta rade-radin da wasu kafafen yada labarai ke yadawa na cewa Sanata Yari na da hannu wajen kafa sabuwar jam’iyyar siyasa”.