Neman Mafita: Gwamnonin Najeriya Sun Yi Taro Ranar Laraba

A ranar Laraba ne gwamnonin jihohi 36 na Najeriya suka gana domin tattauna a kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi jihohinsu da kuma kasa baki daya.

Jigo cikin batutuwan da gwamnonin suka tattauna a kai shi ne kudirin sabuwar dokar nan da za ta ba wa majalisun dokoki da bangaren shari’a na jihohi ‘yancin kai a fannin sha’anin kudi.

Cikin wata sanarwa da kakakin kungiyar gwamnonin NGF, Abdulrazaque Bello-Barkindo, ya fitar a ranar Talata cikin birnin Abuja, ta nuna cewa a ranar Laraba gwamnonin kasar suka gana da juna.

Wannan shi ne zama na 12 cikin jerin ganawa ta nesa-nesa da gwamnonin Najeriya su ka yi ta hanyar bidiyo tun bayan bullar cutar korona a kasar.

A ranar Juma’a, 22 ga watan Mayun 2020, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan wannan doka da ta ba majalisar dokoki da hukumomi shari’a na jihohi damar cin gashin kansu.

Sabuwar dokar mai suna ‘The Executive Order 10, 2020’, za ta ba wa majalisar dokoki da bangaren shari’a na jihohi damar samun kudadensu kai-tsaye ba tare da ya bi ta hannun gwamnonin ba.

A karkashin wannan sabuwar doka, Buhari ya ba wa Ofishin Akanta Janar na kasa umarnin cire wa majalisar dokoki da bangaren shari’a kudaden su daga asusun duk wata jiha da ta ki bin wannan umarni.

Domin gano ina suka dosa, Bello-Barkindo ya ce, ganawar gwamonin ta fara ne da misalin karfe 2.00 na ranar Laraba, 8 ga watan Yuli.

Ya kuma yi bayanin cewa, dukkanin gwamnonin jihohi 36 na kasar sun halarci zaman suna zaune a jihohinsu ta hanyar bidiyo.

Sauran batutuwan da gwamnonin suka tattauna a kai kamar yadda Barkindo ya bayyana sun hadar da matakan ceto tattalin arzikin kasar da ke kan gabar shiga cikin matsi.

Gwamnonin sun mayar da hankali musamman ga Hukumar zuba jari ta Najeriya, NSIA, domin tabbatar da tattalin arzikin kasar ya daidaita har zuwa lokacin da annobar korona za ta gushe.

Sai kuma batutuwan da suka shafi dawo wa da wasu jihohi biyar kudaden da suka kashe wajen aiwatar da wasu manyan ayyuka na gwamnatin tarayya.

Jerin jihohin sun hadar da Ribas, Bayelsa, Cross River, Ondo, da kuma Osun.

Barkindo ya ce gwamnonin sun yi bita kan harkallar cin hanci da rashawa a jihohinsu bisa la’akari da rahotannin da hukumar kididdiga ta kasa NBS ta fitar.

A yayin taron, karamin ministan ma’adanan man fetur, Timipre Sylva, ya gabatar da jawabai kan batutuwan da suka shafi kamfanin sarrafa iskar gas na kasa (NLNG) da kuma shirin fadada kamfanin (NGEP).

Labarai Makamanta

Leave a Reply