Neman Kusanci Ga Allah: Magu Ya Koma Kwanan Masallaci

Rahoton da muke samu yanzu ya nuna cewa dakataccen mukaddashin shugaban hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC, Ibrahim Magu, ya daina kwana cikin ofishin ‘yan sanda kamar yadda yayi kwanaki hudu da suka shude, ya koma kwana cikin masallaci.

Magu, wanda ke fusktantar bincike gaban kwamitin fadar shugaban kasa karkashin Alkali Ayo Isa Salami, ya koma kwana a Masallacin dake cikin hedkwatar hukumar FCID.

An tattaro cewa an gyara ofishin FCID dake Zone 10, cikin birnin tarayya tun lokacin da aka tsare Magu a wajen. Hakazalika, an tattaro cewa manya a hukumar ‘yan sanda sun gana ranar Juma’a, 10 ga Yuli, domin tattaunawa kan lamarin Magu.

Rahoton yace manyan hukumar yan sanda sun yanke shawarar watsi da shi saboda rashin hadin kansa da hukumar ‘yan sanda lokacin da yake cin mulkinsa a EFCC.

Majiyoyi daga hukumar sun bayyana cewa lokacin da yake mulki, da gayya yake nunawa manyan ‘yan sanda yatsa kuma ya daina halarta zamansu karkashin jagorancin IGP Adamu Muhammad.

Bugu da kari, an ruwaito cewa shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi ministoci da manyan jami’an gwamnati cewa kada su sake a gansu suna masu taimakawa Magu wannan lokacin.

Mun kawo muku rahoton cewa Lauyan Ibrahim Magu, a ranar Juma’a ya bukaci kwamitin fadar shugaban kasa dake bincike kansa ta bashi beli. Ya ce akwai bukatar sakin Magu saboda ‘yan jarida na amfani da damar tsareshi da akayi wajen wallafe-wallafen bata masa suna.

Labarai Makamanta

Leave a Reply