A madadin hukumar gudanarwa ta kamfanin ATAR Communications Nigerian Limited mamallakan gidajen Talabijin da Rediyo na Liberty.
Muna neman afuwa dangane da sanya hoton wannan matashi da aka yi a wani labari da jaridar Muryar ‘Yanci mallakar Kamfanin ta yi amfani dashi a ranar 27 ga watan Yunin 2022 mai taken ” Kano: Kotu Ta Haramta Wa Matashi Hawa Doki Na Tsawon Shekaru Uku”
Muna neman afuwar amfani da hoton wannan bawan Allah da muka yi ba shine Abdulsalam Bashir ba wanda Kotu ta hana hawa Doki ba.
Sanarwa Daga Hukumar Gudanarwa