Rahotannin da muke samu na tabbatar da cewar dakarun sojin Nijeriya, haɗin guiwa da haziƙan jami’an kwantar da tarzoma (Mopol) da jaruman ƴan banga, sun yi wa barayi masu garkuwa da mutane da suka addabi al’ummar ƙaramar hukumar Mariga da ke waye ruwan wuta.
Da yammacin yau ne jami’an tsaron suka yi wa ƴan ta’addan ruwan wuta ta sama da ƙasa a dajin Ma’undu dake gundumar Beri. Inda jirgin yaƙi ke sakarwa barayin bama-bamai, yayin da mopol da ƴan banga ke ragargazar barayin ta ƙasa. Kawo izuwa yanzu babu alƙalumman ƴan ta’addan da aka kashe, saidai muna da yaƙinin hukumomin dake da alhakin hakan zasu yi a duk lokacin da suka tattara alƙaluman su a hukumance.
Haƙiƙa jaruman jami’an tsaron mu sun cancanci yabo, da jajirtattun wakilan Jihar Neja irin su Sen. Aliyu Sabi Abdullahi (Baraden Borgu) mai wakiltar Jihar Neja ta Arewa wanda yake tsaye ƙyam domin ganin an shawo kan wannan matsala. Kuma wannan mataki da gwamnati ta ɗauka zai fara sanya kwanciyar hankali a zukatan talakawa, na cewar gwamnati da gaske takeyi.
Allah ya ƙara bamu zaman lafiya.