Rahotanni daga Minna babban birnin Jihar Neja na bayyana cewar Darakta Janar na hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar ta ya ce an sanar da Gwamna Abubakar Sani Bello halin da ake ciki
Rahotanni daga birnin Minna na Jihar Neja na tabbatar da mutuwar akalla mutum takwas yayin da ake ci gaba da neman wasu ?arin biyar a ruwa, bayan da kwale-kwalensu ya kife.
Mutanen dai na ?o?arin tserewa daga ?auyensu na Galkogo da ke yankin Munya ne sanadin wani hari da ‘yan bindiga suka kai a ?auyen.
Wa?anda suka mutu a hatsarin jirgin ruwan sun ha?a mata biyu da ?ananan yara shida.