Rahotannin daga Minna babban birnin Jihar Neja na bayyana cewar Hukumar Rarraba Wutar Lantarki ta Abuja, AEDC, ta gutsure wutar lantarkin gidan gwamnatin jihar Niger, wutar majalisar jihar da ta babban asibitin Minna da sauransu kan tarin bashin da ake bin su.
Sauran manyan wuraren da ake yankewa wutar sun hada da asibitin kwararru na IBB, gidan ruwa na jihar da sakateriyar jihar.
Wannan shi ne karo na uku da aka yankewa gidan gwamnatin jihar wutar lantarki a wannan shekarar sakamakon yadda suka kasa mutunta yarjejeniyar dake tsakaninsu tun a watan Augusta na biyan kudin da ake bin su.
Idan za a tuna, AEDC ta fara yanke wutar cibiyoyin gwamnatin a ranar 20 ga watan Afirilu kuma ta sake yankewa a ranar 26 ga watan Augusta. A yayin rubuta wannan rahoton, ba a mayar da wutar ofisoshi da sassa da yawa na jihar ba.
An ga jami’an AEDC da tsanika suna kaiwa da kawowa a wurin ofisoshin domin yanke wutar, AEDC tace gwamnati ta ki cika sharadin da aka gindaya mata na biyan bashin sama da N1.8 biliyan kamar yadda ta amince kafin a mayar musu da wuta a watan Augusta.