Sakataren gwamnatin jihar Neja, Ahmed Ibrahim Matane ya yi kira ga ‘yan bindiga da su rungumi tattaunawa, sulhu sannan kuma su ajiye makamansu, domin rungumar zaman lafiya.
Sakataren jihar wanda ya raka malamin addinin Musulunci da ke Kaduna, Sheikh Ahmed Abubakar Gumi don ganawa da ‘yan bindigann ya bayyana cewa gwamnati a shirye take ta tattauna da su, domin neman maslaha.
Kamar dai yadda ‘yan fashin suka ba da sharadin zama lafiya a jihar sun ce akwai bukatar gwamnati ta saki mutanensu da ke hannun jami’an tsaro.
Matane ya yi jawabi ga ‘yan fashin da kwamandojinsu a Dutsen Magaji, karamar hukumar Mariga ta jihar Neja inda ya bukace su da su rungumi tattaunawar zaman lafiya da gwamnati ta fara.
Ya bayyana cewa tattaunawar zaman lafiyar za ta kawo karshen matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta, da samar da tsaro da kwanciyar hankali ga jama’ar jihar.
Matane ya kara yin kira ga Kwamandojin ‘yan Bindigan da su goyi bayan kokarin da gwamnati ke yi na ganin an saki fasinjojin da suka sace na Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Neja da Daliban Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati dake Kagara.
Ya ce za a shigo da shugabannin addinai da sauran masu ruwa da tsaki cikin tattaunawar da ake yi da ‘yan fashi, masu satar mutane, da barayin shanu a shirin samar da zaman lafiya da gwamnati ta fara.
A gefe guda, mun ji cewa Shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Gumi, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ba ‘yan Bindiga da ke son yin sulhu afuwa idan har za a magance matsalar tsaro a yanzu.
Malamin ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin ganawa da manema labarai a Minna, babban birnin jihar Neja.
Wannan ya faru ne bayan malamin ya ziyarci sansanin wasu yan bindiga da ke aiki a jihar Neja.