Neja: Fitaccen Malamin Addinin Musulunci Sheikh Lemu Ya Rasu

Sheikh Lemu ya rasu ne da sanyin safiyar yau Alhamis a birnin Minna na jihar Naija ya rasu yana da shekara 91 a duniya.

Ɗaya daga cikin ƴaƴan marigayin, Nuruddeen Lemu, wanda ya tabbatar da rasuwar mahaifinsu, ya ce idan anjima kaɗan za a soma shirye-shiryen binne shi.

Marigayi Sheikh Lemu ya soma karatunsa na addini da na boko a Najeriya inda daga bisani ya tafi Ingila ya kammala Digirinsa na farko a kan African and Oriental Studies a shekarar 1964 a makarantar da a takaice ake kira SAOS.

Ya kwashe galibin rayuwarsa yana koyarwa musamman a fannin Larabci da Ilimin Addinin Musulunci da kuma Hausa.

Kazalika marigayi Sheikh Lemu mutum ne da ya kwashe tsawon rayuwarsa yana kira ga yin masalaha da sassauci a tsakanin al’umma da kuma bayyana ra’ayinsa akan al’amura ba tare da rufa-rufa ba.

Sheikh Lemu ya bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen kare hakkin mata, haka kuma ya kafa kungiyar Da’awa domin yaƙi da tsattsauran ra’ayi.

Mariyagi Sheikh Lemu ya samu lambobin yabo da dama daga ciki da wajen Najeriya, ciki har da lambar yabo ta ƙasa da ƙasa ta Sarki Faisal na Saudiyya wadda aka ba shi a 2014.

Ya rubuta littafai da dama ciki har da A Book of Fasting, Islam for Africa, The Young Muslim, da sauransu.

A shekarar 2019 ne matar Sheikh Lemu, Hajiya Aisha Lemu, ta rasu tana da shekara 79 a duniya bayan ta yi wata gajeruwar jinya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply