Neja: Ba Zan Biya Ku?in Fansar ?aliban Da Aka Sace Ba – Gwamna

Gwamna Abubakar Sani-Bello na jihar Neja ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta biya kudin fansa ga masu satar yaran makarantar Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kangara ba, karamar hukumar Rafi ta jihar.

Bello ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba, bayan sace wasu dalibai da ma’aikatan Kwalejin a daren Talata.

Idan ba a manta ba jaridar muryar ‘yanci ta kawo maku ruhoton yadda wasu yan ta’adda suka sace dalibai a makarantar kwana na gwamnati dake kagara.ko karshen shekarar data gabata anyi garkuwa da daliban kwalejin kimiyya da fasaha ta gwamanati dake karamar hukumar kankara ta jihar katsina wanda sai daga baya daliban suka samu ‘yancin Kansu.

Related posts

Leave a Comment