Neja: An Gar?ame Uwargidan Da Ta Kashe Amaryarta A Kurkuku

Kotun majistare mai zama a Minna ta garkame Amina Aliyu da wasu mutane uku bisa zargin kashe kishiyarta.

A cewar rahoton da ‘yan sanda suka gabatar a gaban alkali, binciken ‘yan sanda ya zargi uwargida Amina Aliyu da hada kai da wasu mutane uku inda bayan dukan kawo wuka da suka yiwa marigayiya Fatima, amaryar da ba ta wuce kwanaki hamsin da takwas da aure ba, a ranar talatar 23 ga watan maris din wannan shekarar, sun kuma yi yunkurin cinna wa gawar marigayiyar wuta, inda hakan bai samu nasara ba.

Ita dai marigayiyar Fatima ta cimma ajalinta ne bayan taron dangin da uwargidan ta jagoranta suka afka mata, inda bayan sun bubbuge ta suka kuma yi nasarar karya wasu gabubban jikinta.

Ita dai uwargida Amina da ta jagoranci yin aika-aikar ba ta wuce sati uku da haihuwar Da namiji ba, kotun ta iza keyarta ne da wasu mutum uku da ake zargi da hannu a aika-aikar da suka hada da Aisha Muhammad, Zainab Aliyu da Fauziya Rabi’u kamar yadda sashen binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan ta gudanar da binciken ta ranar laraba 31 ga watan maris da ya gabata.

Kamar yadda binciken farko ya tabbatar uwargida Amina Aliyu da marigayiya Fatima Aliyu dukkan su matan mutum daya ne da ke zama a Mandela cikin unguwar Sauke-Kahuta a Minna.

Lokacin da ake karanta wa Amina Aliyu laifin zargin da ake mata, an fada mata cewar ta bar shiyyarta dauke da tabarya inda ta afka wa amaryarta a kai ba tare da laifin komai ba. Inda ta fadi na take a kicin cikin jini, sannan ke Amina Aliyu, Aisha Muhammad da Zainab Aliyu da Fauziya Rabi’u kuka dauki gawarta zuwa falon amaryar, inda kuka yi yunkurin cinna wa gawar wuta da nufin cewar gobara ce ta yi sanadin mutuwarta.

Mai gabatar da karan ya bayyana cewar ranar talata 23 ga watan Maris, na wannan shekarar, Bello Lawal da ke Gwari Motors a hanyar Bosso ya ruga zuwa ofishin ‘yan sanda da ke Tudun-wada Tunga Minna ya shaida masu cewar wasu mutane hudu har da Amina sun kashe Fatima Aliyu.

ASP Ahmed Daudu Kongwama na rundunar ‘yan sandan yace zarge zargen da ake yi ma wadanda ake zargin za a iya hukunta su ne bisa dokar Penal court ya shafi sashi 97 da 221.

Bayan kotun ta karanta ma wadanda ake zargin laifukan da ake zargin su da shi, ba ta tsaya sauraren bangaren su ba ta rufe shari’ar ne dan cigaba da yin bincike.

Alkalin kotun majistaren, Nasiru Mu’azu ya nemi ‘yan sandan da su cigaba da bincike kan faruwar lamarin, inda ya tunkuda keyar Amina Aliyu da Aisha Aliyu wadanda ake da su kasance gidan gyara hali yayin da Zainab Muhammad da Fauziya Rabi’u su kasance gidan horar da yaran da ba su balaga ba.

Za a cigaba da sauraren karar ne ranar 27 ga watan Afrilun wannan shekarar dan jin matakin kotun na gaba.

Mahaifan mamaciyar dai sun bayyana cewar ba zasu yafe wannan kisan gillar da aka yiwa ‘yarsu ba, duk wanda ke da hannu a kisan sai sun tabbatar da an hukunta shi.

Related posts

Leave a Comment