Gwamnatin Jihar Neja Ta Dakatar Da Wani Malami Da Ake Zargin Ya Kware Wajen Zagin Sahabbai Daga Wa’azi Da Limanci
Labarin dake shigo mana shine an dakatar da Malam Adamu Minna da ake zargin yana kafurta Sayyidina Umar da sauran Sahabban Manzon Allah SAW daga dukkan wa’azi ko limanci na sai baba ta gani a Jihar Neja.
A labarin da ya riske mu, an cinma yarjejeniyar dakatarwar ne da hadin gwiuwar dukkan bangarorin addini musamman mabiya Darikar Tijjaniya da mabiya Izala wadanda suka yi ruwa da tsaki wajen ganin an dakatar da wannan
Malamin.
Lamarin ?atanci ko cin mutuncin Sahabban Manzon Allah wani lamari ne dake nema zama ruwan dare yanzu musanman a yankin Arewacin Najeriya, inda ake samun wasu mutane dake ikirarin malamta amma basu da wani aiki sai cin zarafi gami da ?atanci ga Sahabban Annabi.