An ambaci sunayen mutum goma sha biyar cikin zargin naira biliyan 5.778 da ya bata na kudin fansho a jihar Neja daga 2009 zuwa 2012.
Darakta janar na hukumar fansho a jihar, Alhaji Usman Tinau Muhammed, ya bayyana hakan a lokacin wani taron manema labarai.
Ya sanar da dawowar shirin tara wa ma’aikata wani bangare na albashinsu wato Contributory Pension Scheme (CPS)a jihar.
Idan za a tuna, jihar ta dakatar da shirin a 2015 saboda abinda ta bayyana a matsayin matsin lamba a gwamnatin wancan lokacin a jihar.
“Wani rahoton sashin binciken kudi ya tabbatar da cewar kudin fansho naira biliyan 5.778 ya bata kuma hakan ya kasance ne saboda kudin bai bi ta hukumar fansho ba.
“An kuma ambaci sunayen mutum goma sha biyar a rahoton kuma duk wani da aka gano za a gayyace shi domin tattaunawa kan lamarin.
“Za mu tattauna da mutanen domin a dawo da arzikin jihar daga wajensu.
“Za kuma a tura lamarin zuwa ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) domin ci gaba da bincike” in ji shi.
Kan dawowar shirin CPS, shugaban hukumar ya bayyana cewa tsohon shirin fanshon ya kasance tattare da tarin matsaloli.
Ya kuma bayar da tabbacin cewa a karshen ritaya, ma’aikata za su samu dukkanin kudin sallamarsu a dunkule da kuma kudin fansho duk wata a kan lokaci.
Ya yi bayanin cewar jihar za ta dawo da shirin ne sakamakon shawarar da kwamitin da gwamnatin jihar ya kafa karkashin jagorancin mataimakin gwamna ya bayar.
“Ragi don shirin CPS ya fara daga watan Yunin 2020 kuma tsarin ya ware ma’aikata daga 1992 har zuwa kasa. Hakan na nufin zai fara ne da ma’aikata daga 1993.
“Wannan tanadin zai kasance 7.5% daga ma’aikaci sannan 10.5% daga gwamnatin jihar” in ji shi.
A cewar Muhammed, a watan Disamban 2019, jihar na da sunaye 8,633 a tsohon shirin fansho din a matakin jihar yayinda kananan hukumomi ke da 7046.
Ya kara da cewar a CPS, akwai sunaye 22,000 na ma’aikatan jiha yayin da har yanzu suke gwagwarmayar samun sahihin sunaye na karamar hukuma cewa banbancin ba zai kasance mai yawa ba amma an yi kiyasinsa a kimanin 25,000.
Domin gudun zamba a sabon shirin, shugaban ya ce ma’aikatar kudi, hukumar kananan hukumomi, ma’aikatar karamar hukuma da SUBEB ne za dunga cire kudaden, sannan a tura zuwa hukumar fansho domin sanya shi a asusun fansho.
Ya kuma yaba ma gwamnan jihar, Alhaji Abubakar Sani Bello kan bayar da izinin dawo da shirin, cewa yana daya daga cikin allawaran da ya dauka a kamfen dinsa na biyu.