Neja: An Bankaɗo Cibiyar Azabtar Da Yara A Suleja

‘Yan sanda sun gano wata cibiyar da ake cutar da yara da cin zarafin su da sunan Almajiranci a yankin Sabon Angwa Kwamba na karamar hukumar Suleja.

Karamar hukumar Suleja tare da masarautar tun daga lokacin suka hada karfi da ‘yan sanda don tura yaran tare da malamin mai cin zarafin su zuwa Minna.

Don haka karamar hukumar Suleja ta bukaci jama’a da su kai rahoton ire-iren wadannan munanan ayyuka ga hukumomi domin tabbatar da doka ba tare da wani bata lokaci ba. Ta hanyar yin haka, za ku taimaka wa gwamnati a yakin da take yi na fataucin yara da cin zarafin yara.

Labarai Makamanta

Leave a Reply