A safiyar ranar Asabar ne aka tabbatar da sako daliban Makarantar Sakandare ta Kagara dake yankin ?aramar Hukumar Rafi ta Jihar Neja daga hannun ‘yan bindigan da suka sace su.
Sakatariyar yada labaran gwamnan jihar, Mary Noel Berje, ta bayyana cewa gwamnan ya karbi bakuncinsu a gidan gwamnatin jihar dake, Minna. Ta bayyana hakan a jawabin da ta saki ranar Asabar a shafinta na Facebook.
A cewarta, gwamna Bello ya godewa Allah bisa nasarar cetosu daga hannun miyagun. Ya shawarci daliban kada su gajiya wajen neman ilimi kuma su dauki wannan matsayin ibtila’i na rayuwa.
Ta kara da cewa cikin mutum 38 da aka saki, 24 dalibai ne, 6 malamai ne, kuma 8 yan uwan malaman ne. Kuma dukkanin su suna samun kulawa daga jami’an kiwon lafiya.
An ruwaito cewa dalibai tare da malaman kwalejin kimiyya ta Kagara da ke jihar Neja sun isa babban birnin jihar, Minna. Dalibai 27, malamai 3 tare da wasu mutum 12 ne aka sace yayin harin da aka kai makarantar.
A faifan wani bidiyo da aka sanya ta kafafen sadarwa an ga daliban suna fitowa daga dajin. An gano cewa an nadi bidiyon a wurin makarantar sakandare na Attahiru da ke Madaka a jihar Neja.
Rashidah Abdul Rahman ‘yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ?angaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Source: Legit TAGS: HAUSA NEWS TRENDING NEWS New wife loading: Hilarious reactions as BBNaija’s Nengi pays courtesy visit to Ned Nwoko 12 hours ago Inside Mike Tyson’s incredible 52-room mansion he sold to rapper 50 Cent for £3.3m 15 hours ago Panic in Oyo as OPC members arrest notorious kidnapper Wakilu Isiaka Muhammadu, 3 others an hour ago Pretty lady rolls her waist, makes quick leg moves as she dances, video sparks reactions 13 hours ago Reincarnation: Woman gives birth, says baby looks like her brother who died years ago, shares photos of them 10 hours ago Young man carries 2 sisters on top very heavy weight bar, they dance on his shoulder, video goes viral 1