Hukumar NDLEA ta fitar da jerin sunayan wadanda suka yi nasara da za a dauka aiki, su duba shafinta na yanar gizo a www.ndlea.gov.org domin ganin bayanin abubuwan da ake bukata daga gare su
Sannan za a fara tantance wadanda suka yi nasara daga ranar 10 zuwa 23 ga watan Janairun 2021 a Jihar Plateau.
Hukumar Hana Fataucin Miyagun Kwayoyi na Kasa, NDLEA, ta fitar da jerin sunayen wadanda suka yi nasara cikin masu neman shiga aiki a hukumar.
Mai magana da yawun rundunar, DCN Jonah Achema ne ya bayyana hakan ga manema labarai ayau Juma’a a Abuja,