Nasiha Ga Matasa Game Da Shaye-Shaye

Daga Muhammad Sani Yusuf Nassarawa

Don Allah Karka Saukemin caji, wannan Itace Kalmar da Wanda yasha kayan Maye ke fadi alokacin da yayi dif wato ya Dauke wuta.

Wannan Kalmar da Makamantansu itace ke fitowa daga Bakunannsu yayin da Wani ke Musu Magana ko Kuma ya Nemi su Aikata wani abu na Daban Wanda Dole Sai Sun Tashi Daga Inda Suke Kafin su iya Aiwatar da Wannan abin, Misali kamar Fita Daga Daki Zuwa Waje, Ko Yi Musu Tambaya akan Wani Abu Daban Dadai Makamantansu,

Wani Tuntube dadin gushi shine, da zarar Matasan Sunyi Mankas da Kayan Maye, To Hatta Abinci bai Damesu ba, ko wani Abin sha, Domin kuwa suna Masa Kallon idan Sun ci ko sun sha Cajin da Suka yi zai Sauka, Idan ka Tambayesu cewa Menene Wannan Cajin da zai Sauka ? Sai Kaji Sunce Maka Baza ka ganebane, Sufa Yanzun Suna Cikin Sulo ne, Ko Suce a Sarauta Suke Jin kansu,

Kaji fa, Wai Sarauta, Ko Wacce Irin Sarauta ce Wannan? Oho,

Lallai Matasanmu Lokaci Yayi da ya kamata kuyi karatun ta natsu, domin kufa ba kananan mutane bane, kunada Matsayi mai Girma, sai dai idan baku gano ba.

Ku lura mana da yadda wasu matasa daga cikinku suka daukaka sakamakon basa shan komi na Shaye shaye, kuma sun tsaya ne sukayi karatu har suka kai matsayin da suke burgeku.

Da Wannan kadai ya isa Matashi ya Fahimci cewa Shaye-Shaye baya kai mutum ga cin nasara a rayuwa, illama ya tsundumaka cikin halin kunci da kuma da na sani wanda masu iya magana ke cewa keyace kuma a baya take,

bazan gusheba ina kara fadakar da matasanmu maza da mata cewa, rayuwarsu tanada muhimmanci ga ci gaban kasa, amma ba a bangaren sha da ta’ammuli da miyagun kwayoyi ba,

Don Haka Ku Hankaltu, Ku lura, Kana ku gane abinda Nasihar da ake muku,

Fatanmu anan Shine Allah Yasa Muku Albarka Sannan Ya Shiryar da Dukkan Matasanmu Masu Shaye-Shaye.

Related posts

Leave a Comment