Wasu yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba, amma ana zargin masu satar mutane ne suna garkuwa da su, sun ?addamar da hari akan wasu bayin Allah Masallata, sannan suka yi awon gaba da mutane 17, a harin da suka kai babban masallacin garin Gwargwada-Sabo da ke yankin Gadabuke na jihar Nasarawa.
Majiyarmu ta gano cewa daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su har da wasu maaikatan dakin adana takardu na Jamiar Ahmadu Bello da ke Zariya, cikin mata uku da maza 13 da akayi awon gaba da su.
Wani mazaunin yankin, mai suna Usman, ya ce lamarin ya faru ne a daren Talata lokacin da Musulmai ke gudanar da sallar Ishai.
Yana mai cewa Yan bindigar sunyi ta harbe-harbe ta bangarori daban-daban, a dai-dai lokacin da wasun su suka kewaye masallacin, inda sukayi awon gaba da mutanen 17 cikin daji.
Usman yace, maharan sun ware limamin masallacin garin da kananan yara a gefe guda, kafin awon gaba da mutanen.
An ruwaito cewa Iyalan mazauna garin sun samu tattaunawa da yan bindigar da suka bukaci naira miliyan daya kan kowane mutun a matsayin kudin fansa, bayan da a ranar farko suka bukaci miliyan 50 kan kowane mutun guda.