Rundunar ?an sandan jihar Nasarawa ta ce wasu ?an bindiga sun harbe shugaban ?ungiyar makiyaya ta Miyetti Allah na jihar da kuma shugaban ?ungiyar na ?aramar hukumar Toto.
Rundunar ta tabbatar da kashe su a cikin wata sanarwar da kakakinta Ramham Nansel ya fitar a ranar Asabar.
Sanarwar ta ce ana tunanin ?an bindiga makiyaya ne suka kai wa shugaban Miyetti Allah na jihar Mohammed Hussaini hari suka harbe shi.
?an bindigar sun kuma kashe shugaban ?ngiyar ta Miyetti Allah na ?aramar hukumarToto a kasuwar Garaku.
Sanarwar ta ce bayan samun labarin a ranar Juma’a da yamma, kwamishinan ?an sanda na jihar Bola Longe ya aika da runduna wuraren da aka samu gawawwakin mamatan tare da ?aukarsu zuwa asibiti.