Nasarawa: An Tsinci Gawar Shugaban APC Bayan Garkuwa Da Shi

An tsinci gawar shugaban jam’iyyar APC na jihar Nasarawa, bayan an yi garkuwa da shi. Wata majiya da take kusa da iyalan mamacin ne ta sanar wa majiyarmu haka a ranar Lahadi da rana. Sannan wani shugaban jam’iyyar APC na jihar Nasarawa, wanda bai so a ambaci sunansa ba, shi ma ya tabbatar da mutuwar.

Duk da dai har yanzu jam’iyyar APC ba ta riga ta yi magana ba a kan garkuwa da shi da aka yi ba. Shugaban karamar hukumar Karu, Samuel Akala, ya tabbatar da mutuwar a shafinsa na sada zumuntar zamani ta Facebook.

Dama kafafen yada labarai su sanar da garkuwa da Shekwa da aka yi a ranar Asabar a gidansa da yake Lafia. Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Nasarawa, Dele Longe, ya tabbatar da garkuwa da shi da aka yi da safiyar Lahadi.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Nasarawa, Emmanuel Bola Longe, wanda ya tabbatar da hakan, ya ce ‘yan bindiga masu tarin yawa ne suka tsinkayi gidan shugaban APC. Gidan na kusa da cocin Dunamis da ke Bukan Sidi a Lafia. Sun isa gidan wurin karfe 11 na dare inda suka yi awon gaba da shi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply