Nasarar Uba Sani Nasara Ce Ga Jama’ar Kaduna – Shehu Molash

An bayyana nasarar da zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani na jam’iyyar APC ya samu a zaɓen da ya gabata a matsayin wata nasara ce ga jama’ar jihar gaba ɗaya.

Mataimaki na musamman ga Gwamnan jihar Kaduna kan harkokin siyasa Alhaji Muhammad Shehu Molash ya bayyana hakan a sakon godiya da ya aike wa jama’ar Jihar Kaduna kan nasarar sabon Gwamna Malam Uba Sani.

Molash wanda shine mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC shiyyar Arewa maso yamma, kuma mataimakin darakta na tsare-tsare da harkar yaɗa labarai na kwamitin yaƙin neman zaɓen gwamnan jihar Kaduna a Jam’iyyar APC, yace jama’ar Jihar za su dara da irin salon shugabancin Sanata Uba Sani.

Molash ya godewa dukkanin jama’ar Jihar Kaduna bisa ga zaɓen da suka yi musu, inda ya tabbatar ba su yi zaɓen tumun dare, domin za su ga aiki babu kama hannun yaro domin Malam ne ya tafi kuma Malam ne ya dawo.

Labarai Makamanta

Leave a Reply