Nasarar Da PDP Ke Samu, Na Biyo Bayan Amincewata Ne – Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce bisa ga yarda da amincewar shi ne PDP ke samun nasara a zaɓukan da ke gudana a kasar nan, saboda haka ya dauki alhakin lallasa APC da aka yi a zaben ranar Asabar da ya gabata na gwamnon a jihar Edoi.

Shugaban kasar ya sanar da hakan a gidan gwamnati bayan karbar sabon gwamna jihar Edo, Godwin Obaseki, tare da mataimakinsa Philip Shaibu da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP.

Buhari ya ce a matsayinsa na babban jiigo a jam’iyyarsa, shine yakamata a dora wa laifin komai ballantana a lokacin da aka lallasa su a zabe.

Shugaban kasar ya jaddada cewa, duk da yana da jam’iyya, amma ya zama dole garesa da ya tabbatar da an bi ra’ayin jama’a yayin zaben Shugaba.

“Mun rasa jihohi masu yawa a fadin kasar nan. A saboda haka bana son gujewa wani hakki da ya hau kaina. Ni ne shugaban jam’iyyata a kasar nan. “Ina kokarin tabbatar da cewa an gina jam’iyyar da wayewa ta zamani, bin dokoki da kuma mutunta hakkokin jama’a”

A wani labari na daban, Lai Mohammed, ministan yada labarai da al’adu, ya ce mulkin kasar nan karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari, na kokarin saka kasar nan a hanyar da ta dace.

A yayin jawabi ga manema labarai a ranar Alhamis domin bayyana shirye-shiryen shagalin bikin cikar Najeriya shekaru 60, Mohammed ya ce tun bayan samun ‘yancin kasar, an fuskanci yakin basasa, rikicin siyasa da kuma rashin tsaro.

Labarai Makamanta

Leave a Reply