Nasarar Afirka: Dole Shugabannin Yankin Su Tashi Tsaye Wajen Magance Juyin Mulkin Soji – Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga ɗaukacin shugabannin Afirka da su tashi tsaye wajen dakile aukuwar juyin mulkin sojin domin tabbatar da wanzuwar dimokuraɗiyya.

Tinubu ya bukaci takwarorin nasa da su mutunta ’yancin dimokuraɗiyya da doka-da-oda da kuma wanzuwar siyasa musamman a wannan lokaci da ake fuskantar kalubale kama daga annobar Coronavirus da matsalar tsaro da dumamar yanayi.

Shugaba Tinubu ya yi wannan kira ne a taron tsakiyar shekara na gamayyar Kungiyoyin Haɗin Kan Afirka da na rassan ƙungiyoyin tattalin arzikin ƙasashen yankin Afirka da ke gudana a Nairobi, babban birnin ƙasar Kenya.

A cikin kunshin bayanan da Babban Sakatare a Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Adamu Ibrahim Lamuwa ya gabatar, Tinubu ya buƙaci mahukuntan ƙasashen na Afirka da su tabbatar sun mutunta batun sake sabunta mulkin dimokuraɗiyya.

Shugaban Najeriyar wanda ya kasance sabon shugaban kungiyar ECOWAS, ya ce ya kamata a yi watsi da batun juyin mulki a faɗin nahiyar, musamman ma wannan lokaci da ake fama da rashin tsaro da sauyin yanayi da kuma annobar korona.

Ya ce abin takaici ne ganin cewa duk da kasancewar Yammacin Afirka sahun gaba wajen ɗabbaka dimokuraɗiyya da kuma kyakkyawar shugabanci, ita ke gaba a yankin wajen amfani da hanyoyi da suka saɓa wa kundin tsarin mulki don sauya gwamnati.

Ya kuma yi gargaɗin cewa yawaitar kifar da gwamnatoci da ake samu a Afirka, na barazanar kawo rashin zaman lafiya da tsaro, da janyo talauci da ɗaiɗaita mutane wajen raba su da muhallansu.

“Tsakanin 2020 zuwa yanzu, Afirka ta fuskanci juyin mulki guda shida da kuma guda uku wanda ba a samu nasara ba. Hakan na janyo tarnaki ga tsarin dimokuraɗiyyar mu a Afirka.

“Don haka, na ke kira ga ɗaukacin shugabannin Afrika da su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun mutunta ƴancin dimokuraɗiyya da kuma doka-da-oda don tabbatar da ɗorewar siyasa a nahiyar,” in ji Tinubu

Labarai Makamanta

Leave a Reply