Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Najeriya Za Ta Rage Yawan Lantarkin Da Ta Ke Ba Kasashe Makwabta

images 2024 03 14T070645.613

Hukumar kula da wutar lantarki ta ?asa (NERC) ta umarci kamfanin samar da wutar lantarki na ?asar ya rage lantarkin da yake bai wa ?asashe ma?wafta domin bun?asa samar da wutar lantarki a cikin gida.

A cikin wata takardar umarni da hukumar ta fitar a ranar Juma’ar da ta gabata, ta ce tsarin da kamfanin samar da wutar lantarki ga ?asashen ?etare ke bi a halin yanzu ya jawo jefa ‘yan Najeriya cikin wahala.

Hukumar ta ?ayyade cewa kashi 6 cikin 100 na wutar da ake samarwa ne kawai za a fitar da su ?asashen ?etare na tsawon watanni shida masu zuwa, daga ranar 1 ga Mayu.

Akwai yarjeniyoyi da Najeriya ta ?ulla na samar da wutar lantarki ga ?asashen Afirka da ke makwabtaka ita.

Ana yawan samun katsewar wutar lantarki a Najeriya saboda karancin wutar amma abin ya ?ara kamari a ‘yan kwanakin nan.

A baya-bayan nan ne kamfanonin samar da wutar lantarki suka ?ara ku?in lantarki ga wasu kwastomomin cikin gida da ke samun wutar lantarki na tsawon sa’o’i 20 a kullum.

Exit mobile version