Najeriya Za Ta Karbi Bashin Dala Biliyan 2.2 Daga Bankin Duniya

images 2024 03 14T070645.613

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Gwamnatin tarayya na shirin karbar kusan dala biliyan 2.2 daga bankin duniya

Ministan Kudi, Wale Edun ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a karshen ayyukan Najeriya a taron bazara na Bankin Duniya/International Monetary Fund a birnin Washington DC na kasar Amurka A Jiya Asabar.

Da yake magana kan hanyoyin samar da kudade na kasa da kasa ga tattalin arzikin Najeriya, Edun ya lissafa kudaden da kasashen waje ke aikawa da su waje, da jarin kasashen waje, da kayayyakin aiki daga bankin duniya da sauran abokan huldar ci gaban kasa da kasa.

Ya kuma bayyana kokarin da bangaren kasafin kudi na tattalin arzikin kasar ke yi wajen yabawa sauye-sauyen manufofin hada-hadar kudi da babban bankin Najeriya ya yi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply