Gwamnatin Najeriya ta shiga sabuwar yarjejeniya da gwamnatin jamhurriyar Nijar na fara shigo da man fetur birnin Zinder.
The Nation ta ruwaito cewa Ministan arzikin man fetur na Najeriya, Temipre Sylva, da Ministan man jamhurriyar Nijar, Mr. Foumakoye Gado, ne suka rattafa hannu kan yarjejeniyar.
“Gwamnatin tarayyar Najeriya da Jamhurriyar Nijar ta rattafa hannu kan yarjejeniyar sufuri da ajiyar arzikin man fetur,” ma’aikatar arzikin mai a Najeriya ta bayyana a wani jawabi.
Bayan tattaunawa da aka kasance anayi tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da shugaba Mahamdou Issoufou, na tsawon watanni hudu yanzu, kamfanin NNPC na Najeriya, da Societe Nigerienne De Petrole (SONIDEP), na Nijar sun amince da wannan harkalla.
Matatar man kasar Nijar Soraz dake Zinder, kimanin kilomita 260 da iyakan Najeriya, na da ikon tace kimanin gangan mai 20,000 a rana.
Gaba daya al’ummar kasar Nijar gangar mai 5000 a rana suke bukata, kuma suna da raran ganga 15,000 da suke bukatar sayarwa.
A jawabin da Garba Deen Muhammad, hadimin ministan man Najeriya ya saki, yayi bayanin cewa shugaban kamfanin NNPC, Malam Mele Kyari, da Dirakta Janar na SONIDEP, Mr. Alio Toune, ne suka rattafa hannu.
Sun yi hakan ne karkashin jagorancin Ministan man Najeriya,Çhief Timipre Sylva; Ministan man Nijar, Mr. Foumakoye Gado; da sakataren kungiyar kamfanonin man nahiyar Afrika (APPO), Dr Omar Farouk Ibrahim.
Jawabi bayan taron rattafa hannun, Sylva ya bayyana farin cikinsa bisa wannan cigaba, yace haka zai kara dankon zumuncin kasuwancin dake tsakanin kasashen biyu.
Kuna ganin wannan koma baya ne ga najeriya a matsayin ta na giwar afruka ko kuwa hakan cigaba ne musamman a harkar kasuwancin kasashen biyu?
Ku cigaba da kasancewa damu a shafin mu na www.muryaryanci.com domin samun ingantattun ruhotanni da dumi dumin su