Najeriya Za Ta Cimma Burin Fitar Da Adadin Man Fetur A Kasuwannin Duniya


Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ƙaramin ministan man fetur Timipre Sylva ya sanar da cewa zuwa mayun shekara mai zuwa, Najeriya za ta cimma burin Kungiyar Kasashen Duniya masu azrikin man fetur OPEC domin fitar da gangar mai miliyan daya da dubu dari takwas.

Wata sanarwa da mai ba ministan shawara kan harkokin yaɗa labarai Horatius Egua ya fitar, ministan ya ce Najeriya za ta yi iya kokarinta domin ƙara tsaurara tsaro kan manyan hanyoyin da bututun mai na ƙasar suke da kuma toshe duk wani wuri da yake yoyo a bututan.

Karamin ministan man fetur ɗin Timipre Sylva ya bayyana cewa tun asali dalilin da ya sa Najeriya ta kasa cimma muradun kungiyar OPEC ba wai saboda ta kasa haƙo ɗanyen man fetur ɗin bane, amma saboda kamfanonin da ke haƙo man ba su son tura ɗanyen man ta bututan ƙasar saboda kada su rinka tafka asara.

Ya bayyana cewa da zarar an ƙara tsaurara tsaro an tabbatar bututan suna lafiya ba su huje ba, za a ci gaba da tura man fetur ɗin domin cimma muradin OPEC din na samar da ganga miliyan daya da dubu dari takwas a kullum.

Mista Bala Zaka wanda mai shari ne kan makamashi ya ce akwai yiwuwar kalaman da karamin ministan ya yi za su iya zama gaskiya

Haka kuma ya ƙara jaddada cewa kamfanonin da ke haƙar mai su ma za su samu tagomashi idan aka magance matsalar fasa bututan mai aka tsaurara tsaro.

Ministan ya ƙara jaddada cewa man da ƙasar ke samarwa ya ƙaru fiye da a baya inda ya ce a halin yanzu ana samar da sama da ganga miliyan ɗaya.

Ministan ya bayyana cewa gyaran da ake yi a halin yanzu na matatun man Fatakwal da Warri da kuma shirin da ake yi na gyaran matatar Kaduna da bude matatar dangote da ke shirin fara aiki duk wani tabbaci ne da Najeriya ke da shi na samar da wadataccen mai

Labarai Makamanta

Leave a Reply