Najeriya Za Ta Bi Kadin Kisan Ɗalibi Ibrahim Khaleel A Ƙasar Cyprus

Shugabar hukumar ‘yan Najeriya a kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, ta bukaci a kwato hakki biyo bayan mutuwar wani dalibi dan Najeriya mai shekaru 25 a arewacin Cyprus, Malam Ibrahim Khaleel Bello, da sauran al’ummanta da aka kashe a kasar.

Hukumar ta bayyana a wasu jerin wallafa da ta yi a twitter cewa “Ibrahim Khaleel Bello na daga cikin kimanin ‘yan Najeriya 100 da aka kashe cike da ban al’ajabi daga 2016 zuwa 2020 ba tare da hukunta ko daya daga cikin makasan ba.”

Misis Dabiri ta yi wannan roko na kwato hakkin ne biyo bayan wani korafi daga Justis Amina Ahmad Bello, Mai Shari’a a babbar kotun jihar Kaduna kan mutuwar ban mamaki na danta.

Ya kasance a shekararsa ta uku inda yake neman digiri a fannin injiniya a jami’ar Girne American a Girne (Kyrenia), Jumhuriyar Turkiyya na arewacin Cyprus( TRNC).

Dabiri-Erewa ta yi kira ga iyaye da su daina tura yaransu arewacin Cyprus domin Majalisar Dinkin Duniya bata san da ita ba illa Jumhuriyyar Turkiyya, inda ta kara da cewar Najeriya bata da alakar daflomasiyya da wannan kasa.

Ta ce lallai ya kamata a sanya wannan kasa a baƙin littafi sakamakon yawan daliban Najeriya da suka yi mutuwar ban al’ajabi a kasar ba tare da gurfanar da wani ko biyan diyya ba.

Ta ba tawagar karkashin jagorancin Bello tabbaci cewa hukumar NIDCOM za ta yi aiki da ma’aikatar shari’a, hukumar Najeriya a Turkiyya da sauran hukumomin da ya kamata domin tabbatar da an yi adalci.

Ta kara da cewar : mutuwar Ibrahim Khaleel Bello ya zama izina na kawo karshen ci gaba da kashe-kashen daliban Najeriya a wannan kasa.

Dabiri ta bayyana cewa mafi akasarin fanonnin da iyayen Najeriya ke tura ‘ya’yansu domin karantowa a jami’o’in arewacin Cyprus basu da lasisi kuma sai a kare da kashe masu yara, ba a kai rahoton yawacinsu ba.

Ta ce: “Lokaci ya yi da za mu sanya dukkanin jami’o’in arewain Cyprus a baƙin littafi sannan mu shawarci ɗalibanmu daga neman gurbin karatu a can domin hatsari ne ga rayuwarsu da makomarsu a nan gaba.”

Ta kara da cewar ofishin Atoni Janar na tarayya ta rigada ta sanar da lamarin ga ‘yan sandan kasa da kasa domin ci gaba da bincike.

Justis Amina Ahmad Bello, mahaifiyar marigayin ta ce tana so a bi hakki ne ba wai don saboda danta ba illa saboda sauran daliban Najeriya wadanda aka kashe a kasar.

Ta yi bayanin yadda aka kashe mata ɗa sannan hukumomi a arewacin Cyprus suka yi rufa-rufa da hukumomin jami’ar wadanda suka yi ikirarin cewa shi ya kashe kansa.

Sun yi ikirarin cewa ya fado ne daga bene mai hawa bakwai.

Ta ce lallai sai dai a yi bincike sannan a gurfanar da dukkanin wadanda ke da hannu a ciki domin babu abun da ke nuna ɗanta ne ya kashe kansa.

Justis Bello ta ce ‘yan sa’o’i kafin a kashe mata ɗa ta yi magana da shi, sannan ya nuna tsoro game da rayuwarsa a jami’ar.

Ta ce: “Ban yarda cewar hatsari ko kisan kai bane domin naje Cyprus sa’o’i 24 bayan faruwar lamarin sannan na je wajen ajiyar gawawwaki inda babu kurzunu ko ciwo a jikinsa. Kawai ina zargin cewa an kashe mani Ɗana ne.”

Ta ce ‘yan sa’o’i kafin mutuwar yaron, ya aika mata sako ta WhasApp cewa : “Mama, don Allah ina so na dawo gida. Wallahi idan na tsaya a nan, mutuwa zan yi ba tare da wani ya damu ba. Kawai ina son dawowa gida. Mama dan Allah ki fahimci cewa nan ba wajen zama na bane.”

Ta yi zargin cewa akwai yiwuwar an kwashe wasu muhimman kayan cikin mamacin domin an farke cikin dan nata kuma gawarsa na dauke da dinki a lokacin da aka sake shi.

Marigayi Ibrahim Khaleel Bello na cikin ‘yan Najeriya 100 da aka kashe a kasar daga 2016 zuwa 2020 ba tare da an hukunta wadanda suka aikata hakan ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply