Najeriya Ta Yi Asarar Dala Biliyan 12 Sakamakon Rikicin Manoma Da Makiyaya

An samu rahoton asarar akalla dala biliyan 12 a Nijeriya, sakamakon rikicin manoma da makiyaya da ya mamaye sassa daban daban na kasar.

Daraktan kungiyar sa kai ta Mercy Corps, Ndubisi Anyanwu, a ranar Talata ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai jim kadan bayan ganawa da jami’an gwamnati a Makurdi.

“Mun yi kiyasin asarar akalla $12b a kowacce shekara sakamakon rikicin makiyaya da manoma. “Wannan wani babban al’amari ne kuma da zai iya shafar kasar baki daya,” a cewarsa.

Anyanwu ya kara da cewa akwai bukatar a mayar da hankali kan rikici tsakanin makiyaya da manoma, yana mai cewa wannan ne ma dalilin da yasa kungiyar ta shiga cikin lamarin.

Ya yi nuni da cewa kungiyar Mercy Corps, da aka samar da ita karkashin hukumar USAID, ta mayar da hankali kan gina zaman lafiya na watanni 60 a Benue da wasu jihohin jihar.

Tun farko, shugabannin kananan hukumomi a jawabansu daban daban sun lissafa rashin aikin yi, rashin ababen more rayuwa daga cikin dalilan haddasa rikicin makiyaya da manoma.

A wani labarin; Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta cafke mutane 45 da ake zarginsu da laifin garkuwa da mutane da mallakar miyagun makamai a sassa daban daban na jihar.

Daga cikin wadanda aka kama, akwai mai shekaru 40 wanda ake zargin ya kware wajen safarar makamai ga ‘yan ta’addan Boko Haram.

Jihar Borno ta dade tana fuskantar matsalolin tsaro, inda aka kashe mutane da dama, ya yin da dubunnai suka rasa muhallansu na gado.

A yayin da jami’an tsaro ke fafutukar dai-daita lamuran tsaro a jihar, a hannu daya kuma ana aikata wasu laifukan a sassa daban daban na jihar. Amma rundunar ‘yan sanda ta jihar Borno ta ce ba za ta sarara ba har sai ta wanzar da zaman lafiya da cafke masu aikata munanan laifuka a jihar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply