Najeriya Ta Talauce Dole Ta Ciyo Bashi Daga Waje – Shugaban Majalisa

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban majalisar Dattijai, Sanata Ahmad Lawal ya bayyana cewa, Najeriya ta shiga jerin matalautan kasashe dan haka dole ta ciyo bashi dan gudanar da ayyukanta na ci gaba.

Ya bayyana hakane bayan ganawa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ranar Alhamis inda suka yi ganawar Sirri.

Saidai yace duk da haka ba zasu rika amincewa da bukatar bangaren zartaswa na karbar bashi ido rufe ba.

Jawabin Shugaban Majalisar ya haifar da cece kuce tsakanin ‘yan Najeriya, inda wasu ke nuna goyon baya ga maganar tashi, yayin da wasu ke suka.

Gwamnatin Buhari a yau dai tana gaba akan sauran gwamnatocin da suka gabaceta wajen ciyo bashi daga waje, wanda a baya lokacin yaƙin neman zabe babban makamin da APC ta yi yaƙi dashi shine sukar lamirin gwamnatin PDP na neman talauta Najeriya da bashi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply