A cikin hudubarsa ta baya-bayan nan ya koka kan yadda Najeriya ta zama kazamar kasa, cike da tarkace, yaudara, karya, cin amana, da kuma rikita-rikita inda duhu ya mamaye komai.
Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 6 ga watan Janairu, yayin da yake gabatar da hudubarsa a babban cocin Katolika na St Joseph, Kaduna, a lokacin da ake gudanar da hidimar Archbishop Peter Yariyock Jatau, Archbishop na Kaduna Catholic Diocese.
Shugaban addinin wanda ya kare kansa a sakonsa na Kirsimeti na 2020 wanda ya haifar da martani, ya dage cewa a matsayinsa na malami ba zai iya yin shiru game da abubuwan da ba daidai ba, ya kara da cewa hakkinsa ne ya kula da birnin.
A cewar Kukah, ya kamata ya daga muryarsa a matsayin mai tsaro a duk lokacin da ya hango hatsari a kasar.
Idan za a iya tunawa Kukah ya yi bayani lokacin bikin Kirsimeti wanda ya jawo suka daga magoya bayan Shugaba Buhari.
Malamin ya siffanta Buhari da nuna kabilanci, ya kara da cewa da a ce dan kudu ne ke mulki a yau, da an yi masa juyin mulki.
Sakon ya girgiza magoya baya da masoya shugaban wadanda suka yi amfani da shafukan sada zumunta inda suka zargi Kukah da ruruta wutar fitina da dumama siyasa.