Najeriya Ta Shiga Matsi Dalilin Kunnen ?ashi Na Buhari – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya wallafa sakon shawarwari ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, bayan tattalin arzikin Nijeriya ya sake karyewa a karo na uku.

“Zuciyata ta yi nauyi sakamakon samun tabbacin mun sake fa?awa ruwa a karo na biyu sanadiyyar mashasharar tattalin arzi?i da Najeriya ta sake fa?awa ciki na ?angin tattalin arziki.

“Eh, tabbas annobar COVID-19 ita ce silar janyo wannan matsala, sai dai, da tuni mun kaucewa wannan hali ta hanyar ta amfani da basira gami da hangen nesa tare da tattala tattalin arzi?in mu.

“Tunda mai afkuwa ta afku, ba ha??in kowa bane tada jijiyar wuya akan batun. Dole mu maida hankulanmu kan nemo mafita.

Najeriya na bu?atar nagartaccen shugabancin da zai ja akalarta zuwa hanyar farfa?o da tattalin arzi?inmu.

“Ba zai yiwu mu na?e hannayen muyi zuru ba. Dole mu ?auki mataki ta hanyar gudanar da abubuwan da suka zama dole, wata?ila matakan su kasance masu zafi da ra?a?i.

“Farawa da kasafin ku?in da aka gabatarwa majalisa a ranar Talata, 8 ga watan Oktoba 2020, baya cikin tsari yanzu.
“Najeriya ba tada ma’adanai ko bu?atar kasafin alatu mai tsada irin wanda shugaban kasa ya gabatar.
“?asa ta tagayyara, amma bata rushe ba. Duk da haka, idan muka cigaba da almubazzaranci, ko da abin da muke samu bai kai gejin da muke nema ba, ?asar zata tashi daga tagayyararriya zuwa rusashiyar ko ?allaliyar ?asa.

“Saboda kaucewa hakan, akwai matakan da ya kamata gwamnati ta dauka cikin gaggawa. “Wannan ya ha?ar da soke tafiyar da ba ta gaggawa da hanzari ba, rage kudin ciyarwar shugabanni, hakura bushasha da jinda?i, dakatar da fita horo a ?asashen waje, hakura da siyo sabbin ababen hawa da gyaran ofisoshi da kuma alawus ?in da bana albashi ba da sauransu,”.

Atiku ya ce lokaci ya yi da ya kamata shugaba Buhari ya bude kunnuwansa, ya saurari shawarwarin da ake bashi a kan hanyoyoyin gyara tattalin arzikin Nijeriya ba tare da la’akari da banbancin jam’iyya ba.

Related posts

Leave a Comment