Najeriya Ta Shiga Jerin Kasashen Da Talakawa Ke Jin Dadi A Duniya

Rahotannin dake shigo mana daga zauren Majalisar ɗinkin Duniya na bayyana cewar Najeriya ce kasa ta 114 cikin jerin kasashe 146 da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da ‘yan kasarsu suka fi jin dadi.

Uganda ta zarce Tanzania da Kenya a jerin kasashen da mutanensu suka fi jin dadi a duniya.

Kenya ce ke matsayi na 119, wanda hakan ke nufin ta kara yin kasa daga matsayi na 86 a bara, yayin da ita kuma Uganda take kasa da Kenya a shekarar da ta gabata da mataki biyu inda take matsayi na 83 .

Tanzaniya ta dawo matsayi na 134 daga na 94 da take a baya.

A jerin sunayen da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, Rwanda ita ce kasa ta karshe da mutanenta suke da karancin jin dadi a kasashen yankin, inda take matsayi na 147.

Ba a sanya sunan kasahen Burundi da Sudan ba cikin jerin kasashen da mutanensu ke jin dadin rayuwa a duniya ba.

Tsubirin Mauritius shi ne na daya cikin jerin kasashen Afrika da mutanensu suka fi jin dadi inda take matsayi na 44 a duniya.

Finland itace ke matsayi na daya a duniya cikin shekaru hudu a jere kenen inda Denmark ke biye mata da Switzerland da Iceland da kuma Netherlands.

Labarai Makamanta

Leave a Reply