Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Ministan Harkokin wajen Najeriya Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, ya yi kira da a ɗauki matakin gaggawa Domin dakile munanan hare-haren da ake kai wa a rikicin I$ra’ila da Falasdinu. Ambasada Tuggar ya kuma tabbatar da goyon bayan Najeriya ga shawarwarin tsagaita wuta na shugaba Joe Biden.
“Ya kamata shugabannin duniya da daukacin al’ummar duniya su amince da kudurin tsagaita bude wuta na Biden don kara kaimi wajen warware rikicin cikin gaggawa da kuma dakatar da mummunan tashin hankali a Gaza da sauran yankunan da ke shafar fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba,” in ji ministan a ranar Lahadin da ta gabata. Sanarwar ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Alkasim Abdulkadir, “Hakanan Yana da mahimmanci, ci gaba da samar da kayayyakin jin kai da ceton rai ga fararen hula.”
Najeriya ta Baiwa Amurka tabbacin goyon bayanta wajen Ganin an kawo ƙarshen tashe-tashen hankula da kuma kawo karshen salwantar rayukan Mutane Shirin Biden Yana bada kyakkyawar hanya zuwa cigaba da kuma yanayin da ake buƙata don zaman lafiya, Inji “Tuggar
Shawarar ta Shugaba Biden ta hada da yarjejeniyar tsagaita bude wuta na dindindin, da karuwar agajin jin kai, sakin wadanda aka yi garkuwa da su, da kuma wani babban shirin sake gina gidaje, makarantu, da asibitoci. Najeriya ta yi imanin cewa shirin Biden shine hanya mafi dacewa ga dukkan bangarorin kuma zai iya hana sake aukuwar munanan abubuwa kamar mutuwar mutane sama da 200 a sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat a Ranar 8 ga watan Yuni.