Najeriya Ta Girgiza Sakamakon Rasuwar Balarabe Musa

Najeriya ta yi matuƙar girgiza sanadiyyar rasuwar Sananne kuma gwarzon ɗan Siyasa Alhaji Abdukadir Balarabe Musa, tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna, wato lokacin da Kaduna take haɗe da Katsina.

Balarabe Musa ya rasu a ranar Laraba da ta gabata bayan fama da jinyar rashin lafiya da ya yi, kuma an gudanar da Sallar Jana’izar shi a babban Masallacin Juma’a na Sarkin Musulmi Bello da ke Unguwar Sarki Kaduna.

‘Yan Najeriya da aka zanta da su dangane da rasuwar jigon siyasar sun bayyana rasuwar Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa a matsayin wani babban rashi ga dimokuraɗiyya a Najeriya.

Balarabe Musa wanda shi ne gwamnan farar hula na farko a tsohuwar jihar ta Kaduna – ya rasu ne a ranar Laraba bayan ya yi fama da jinya.

Ya zama gwamna ne 1979 a ƙarƙashin jam’iyyar PRP, ko da yake an tsige shi a 1981 kafin ya kammala wa’adinsa.

Marigayin na cikin manyan ‘yan siyasar Najeriya da suka taka rawa wajen tabbatar da mulkin dimokuradiyya.

Balarabe Musa ya shafe rayuwarsa a jam’iyyar adawa inda ya ci gaba da taka rawa a harkokin siyasa da bayyana ra’ayoyinsa kan yadda ake tafiyar da Najeriya.

Wane ne Balarabe Musa?

Marigayin na cikin manyan ‘yan siyasar Najeriya masu ra’ayin sauyi da suka taka rawa wajen tabbatar da mulkin dimokraɗiyya ta hanyar nuna rashin amincewa ta zahiri da mulkin soja.

An haife shi ne a watan Agustan shekarar 1936 a garin Kaya dake yankin ƙaramar Hukumar Giwa ta jihar Kaduna, ya yi karatu a cibiyar nazarin harkokin mulki da gudanarwa da ke Zaria da kuma wasu makarantu da ke birnin London.

An zaɓe shi gwamnan jihar ta Kaduna ne a 1979 a ƙarƙashin jam’iyyar PRP, mai rajin ceto talaka daga mulkin danniya. Ko da yake an tsige shi a 1981 kafin ya kammala wa’adinsa.

Amma duk da haka ya ci gaba da taka rawa a harkokin siyasa da bayyana ra’ayoyinsa kan yadda ake tafiyar da Najeriya inda har ya jagoranci wata tafiya ta ƙalubalantar gwamnatin soji ta Marigayi Janar Sani Abacha da zummar ganin an mayar da kasar kan tafarkin dimokuraɗiyya.

Bayan komawar ƙasar kan tafarkin dimokuraɗiyya a 1999, Marigayi Abdulƙadir Balarabe Musa ya zama shugaban CNPP, wata gamayyar jam’iyyun adawar ƙasar na jamhuriyya ta huɗu.

A shekarar 2018, marigayin ya bar harkokin siyasa gadan-gadan saboda dalilai na rashin lafiya inda har ya sauka muƙaminsa na shugaban jam’iyyarsa ta PRP.

Amma duk da haka ya ci gaba da bayyana ra’ayinsa kan yadda ake gudanar mulkin kasar musamman kan batutuwan suka shafi cin hanci da kuma facaka da dukiyar talaka da ya yi fice wajen nuna adawa da su.

Alhaji Balarabe Musa ya rasu yana da shekara 84, inda ya bar ƴaƴa tara, mata uku da maza shida.

Ɗaya daga cikin ƴaƴansa Sagir Balarabe Musa ya ce sun yi rashin mahaifi wanda ya gina su a kan rayuwar tafiyar da jama’a da kamanta gaskiya da hakuri da kuma shugabanci.

Tuni shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya fitar sanarwar ta’aziyya ga al’ummar Najeriya da jihar Kaduna kan rasuwar tsohon gwamnan wanda ya bayyana a matsayin muryar masu rauni.

Yayin da yake addu’ar neman masa gafarar Allah, Shugaba Buhari ya ce marigayin ya yi wani gagarumin tasiri a dimokraɗiyyar ƙasar kuma ya taka gagarumar rawa wajen tabbatar da kyakkyawan shugabanci da ci gaban al’umma da ƴan kasar za su riƙa tuna shi tare da gode masa a ko da yaushe.

Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-rufai ya ce za a tuna Balarabe Musa a matsayin ɗan siyasa mai son ci gaban al’umma wanda kuma ya faɗaɗa hanyoyin samun damarmaki ga talakawa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply