Najeriya Ta Gano Gas Da Ya Haura Zurfin Kafa Tiriliyan 206 A Karkashin Kasa

Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Karamin ministan man fetur na Najeriya Timipre Sylva ya ce kasar ta gano tarin gas da yawansa ya kai zurfin kafa triliyan 206 jibge a karkashin kasa, yayin da ake kokarin hako danyen man fetur.

Jaridun Najeriyar sun rawaito ministan na cewa kasar na iya gano karin gas din da yawansa ya kai zurfin kafa triliyan 600 idan ta mayar da hankali sosai a nan gaba da zummar cimma burinta na fadada harkar gas a kasar.

Ministan ya kuma bayyana shirin fadada samar da iskar gas a matsayin “babbar madafar ci gaban tattalin arziki”.

Najeriya ce kasar da ta fi kowace kasa samar da mai da iskar gas a Afirka.Article share tools

Labarai Makamanta

Leave a Reply