Najeriya Ta Afka Cikin Karayar Arziki Mafi Muni A Tarihi – Hukumar Kididdiga

A karo na biyu tun bayan 2016, Najeriya ta sake afkawa cikin tabarbarewar tattalin arziki, yayin da ake shirin afkawa ramin da shekaru arba’in ba a shiga kunci irin sa ba.

A karo na biyu kenan, tattalin arzikin na Najeriya ya sake tabarbarewa, bayan ya tabarbare shekaru biyar da su ka gabata. Watanni shida kenan Malejin Bunkasar Tattalin Arzikin Cikin Kasa (GDP) ya yi tsaye cancak, ya kasa gaba. A gefe daya kuma sai tiriliyoyin bashi gwamnatin Buhari ke ta kara labtawa kan gadon bayan tabarbararren tattalin arzikin.

Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS), wadda hukuma ce ta gwamnatin tarayya, ta bayyana wannan labari maras dadin ji.

NBS ta ce tsawon watanni shida kenan tattalin arzikin Najeriya ya kasa motsawa gaba. Har yau a kashi 3.62 ya ke, ga shi an shiga wasu wasu watanni uku masu hatsari, ga shi kuma 2020 ta na gab da karewa, sannan kuma za a shiga shekarar 2021 za a shiga, shekarar likimon bashi a wuyan Najeriya.

Baya ga bashin da Najeriya ke kara labtawa kan ta, kusan rabin kudin da Najeriya ke samu a duk wata, ya na tafiya ne wajen biyan basussuka da kuma biyan kudin ruwan basussukan da ba kai ga fara biya ba.

Rahoton Premium Times

Labarai Makamanta

Leave a Reply