Ƙasashe da dama ciki har da Amurka, sun yi wa Najeriya tayin taimakawa wajen ceto daliban Kuriga da aka sace a jihar Kaduna, in ji Ministan yada labarai Mohammed Idris.
A karshen makon da ya gabata ‘yan bindiga suka far wa makarantar firaimre da Sakandare ta Kuriga suka kwashe dalibai sama da 250 a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.
A cewar Idris, gwamnati “na nazari” kan tayin da kasashen suka yi na taimakawa wajen ganin an kubutar da daliban.
Gwamnatin Amurka a cewar AFP, ba ta tabbatar da batun tayin yi ba kuma ba ta yi karin haske a kai ba.
Kalaman Ministan na zuwa ne yayin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa ba za ta biya kudin fansa ba.
‘Yan bindigar da suka sace daliban sun nemi a biya su Naira biliyan daya a matsayin kudin fansa.