Najeriya Na Fuskantar Barazanar Tarwatsewa – Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce akwai yiwuwar tarwatsewar Najeriya idan ba’ayi kokarin toshe barakar dake kunno kai ba.

Yace akwai wadanda zasu iya yunkurin hana toshe barakar, amma idan aka jajirce kuma aka dage da addu’a za’a iya cimma gaci.

Osinbajo yayi wannan jan kunnen ne a ranar Lahadi a Abuja a wata tattaunawa da aka yi da shi, saboda shiryawa shagalin cika shekaru 60 da samun ‘yancin kai na Najeriya.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ne ya wakilci mataimakin shugaban kasar, kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa.

Cikin mutanen da suka samu damar halarta har da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan; kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila; shugaban ma’aikatan tarayya; Folshade Yemi-Esan, manyan sakatarorin gwamnati, mayakan tsaro da sauran manyan mutane.

Labarai Makamanta

Leave a Reply