Najeriya Na Fuskantar Barazana Mafi Muni A Tarihi – Fadar Shugaban Kasa

An bayyana cewar kasa Najeriya na fuskantar wata gagarumar barazana mafi muni a tarihin ta, biyo bayan yadda ?ungiyoyin kabilu a yankin ke han?oron ?allewa daga ?asar, saboda wasu dalilai nasu na son zuciya.

Ministan ya?a labarai da al’adu Lai Mohammed ya bayyana hakan ga manema labarai jim ka?an bayan kammala zaman majalisar zartawa ta kasar wanda ya gudana a fadar shugaban kasar, inda ya ?ara da cewar yana da kyau manyan Najeriya su fahinci muhimmancin ci gaba da kasancewar Najeriya kasa daya.

Ministan ya zargi manyan mutane da ruruta wutar wargajewar kasar, kuma ya yi gargadin cewa za su dauki mafi girman munin sakamako idan Najeriya ta rabu.

A cewarsa, wasu manyan mutane da suka kai matsayin Farfesa ana iya barinsu ba tare da wani zabin da ya wuce yin aiki a gidajen burodi a makwabciyar kasar Togo ko Ghana don kawai su rayu.

“Kalubalenmu ya fi yawa ga masu fada aji, ba wai talakawa ba. Ku je zuwa kauyuka a Najeriya a yau, za ku ga ‘yan Najeriya daga kabilu daban-daban, al’adu da addini suna zaune tare cikin lumana,” inji shi.

“Ya kamata masu fada aji su shige gaba wajen don tabbatar da hadin kan kasar. Amma lokacin da masu fada aji suka fara da’awar kiyayya na kabilanci, mutane suna gaskata su saboda suna tunanin sun fi sani, babu shakka za’a kai ga wani rami wanda za’a gagara fitowa.

“Najeriya na dauke da kaso 70% na al’ummar Yammacin Afirka, kuma idan Najeriya za ta wargaje a yau, za mu mamaye Jamhuriyar Benin, Togo, Nijar da sauran kasashe makwabta.

“Masu fada aji za su sha wahala matuka saboda wasu furofesoshi za su iya komawa aiki a gidajen burodi a Togo don tsira da rayuwarsu kawai.

Mun ga abin da ya faru lokacin da ‘yan Liberiya suka zo nan lokacin yakin basasarsu. “Yana daga cikin damarsu karan-kansu su yi aiki don gyara Najeriya. Yawancinsu suna da fasfo fiye da daya – Na Amurka, Biritaniya, Turai – kuma a farkon tashin hankali, zasu gudu.”

Related posts

Leave a Comment