Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce Najeriya tana da miliyoyin mutane da ke fama da matsanancin talauci. Ya fadi hakan ne yayin da yake jawabi a wani taro a fadar shugaban kasa Abuja.
Ya ce shugabannin da aka zaba basu da amfani indai har basu hada karfi da karfe wurin taimako a kan matsalar nan ba. Ya ce, “Dole ne kowanne shugaba ya fahimci yadda zai tafiyar da mulkinsa.
Idan aka kalli halin da miliyoyin talakawan Najeriya suke ciki, gashi yanzu cutar COVID-19 ta kara dagula komai, talauci da rashin aikin yi sun yawaita. “Kayan masarufi sun yi kaca-kaca, yara kuma basu zuwa makarantu. Idan muka yi shiru kuma muka ki motsawa, mutane da dama zasu rasa rayukansu.”
“Lokaci yayi da mu da aka zaba zamu motsa muyi abubuwan da suka kamata. “Mutanenmu da yaransu na fama da rashin ci, sha ,muhalli, suttura, rashin lafiya da kuma rashin ilimi. “Wajibi ne duk wani mai fada a ji ya zabura, ya kuma tabbatar ya taimakawa talakawa don gudun abinda zai kai ya kawo.”
A wani labari na daban, Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a ranar Lahadi ya nuna fushinsa a kan kame da cin zarafin da jami’an ‘yan sanda suke wa matasa a Najeriya. Mataimakin shugaban kasan wanda ya samu zantawa da Sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu, ya sanar da shugaban ‘yan sandan da ya kawo sauye-sauye da za su canza miyagun ayyukan ‘yan sandan.