Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce abubuwa biyu ƴan Najeriya ke buƙata domin su fita daga kalubalen da ƙasar ke fuskanta Ya ce har sai mutane sun ba gwamnati goyon baya tare da saka yaƙinin cewa komai zai gyaru ne Najeriya za ta shawo kan matsalolinta.
Shettima ya yi wannan jawabi ne a Abuja, a wajen bikin kaddamar da cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa ta Najeriya a ranar Litinin.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, a ranar Litinin, ya bukaci goyon bayan daukacin ‘yan Najeriya a kokarin da ake na magance kalubalen da ke addabar kasar.
Shettima ya yi wannan jawabi ne a Abuja, a wajen bikin kaddamar da cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa ta Najeriya.F
Farfesa Bolaji Akinyemi ne ya kafa cibiyar wadda ke da nufin ba da gudummawa ga tsara manufofin kasashen waje da aiwatar da su a Najeriya.
Da yake jawabi a wajen taron, mataimakin shugaban kasar, ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta amince da cewa Najeriya na fuskantar kalubale. Shettima ya samu wakilcin Hakim Baba Ahmed, mai ba shi shawara na musamman kan harkokin siyasa, inda ya ce:
“Wannan gwamnatin ta yarda da cewa muna fuskantar matsaloli, duk da hakan, muna da yakinin cewa Najeriya za ta fita daga kalubalen da take fuskanta.
“Abubuwa biyu muke da bukata; yakinin cewa komai zai daidaita da kuma goyon baya, abubuwan da suka taimake mu wajen fita daga manyan kalubale a baya.” Ya ce Najeriya na da karfin ikon magance matsalar talauci, abubuwan more rayuwa, bunkasa matasa da ba su ilimi.