Najeriya Ce Ta Uku A Duniya Ɓangaren Rashin Tsaro – Hukumar Ƙididdiga

Najeriya ta zo a mataki na uku a jerin kasashen da ta’addancin ya yi wa katutu a fadin duniya, kamar yadda rahoton ƙungiyar ƙididdigar ta’addanci ta duniya (GTI) ta bayyana.

Rahoton ya bayyana cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon yakin Boko Haram ya nunka daga shekarar 2018 zuwa 2019, zubar da jinin jama’a ya yawalta sosai.

Ƙasar Afghanistan ce a mataki na farko, sai kuma kasar Iraq a mataki na biyu, a jerin kasashen da ta’addanci ya shahara Najeriya ta na mataki na uku, wato tana kafaɗa da kafaɗa da waɗancan ƙasashen.

Rahoton da ƙungiyar ta fitar ya nuna cewa adadin yawan mace-mace sanadiyyar ayyukan ƙungiyar Boko Haram ya ƙaru da kaso 25% daga shekarar 2018 zuwa 2019, fargaba da tashin hankali ya hauhawa a zuƙatan ‘yan Najeriya.

Rahoton ya bada misali da harin da aka kaiwa masu jana’izar gawa a garin Badu Jihar Borno a shekarar 2019 wanda ya kasance mafi muni cikin hare haren ƙungiyar Boko Haram.

Ƙungiyar GTI ta gano cewar, sanadiyyar ƙaruwar masu mace-mace daga hare haren ƙungiyar Boko Haram a Arewa maso gabas ɗin ƙasar, Najeriya itace ƙasa ta biyu da ta samu hauhawar adadin mace mace sanadiyyar ta’addanci da hargitsi.

“Rahoton ya ce an kashe mutane 2,043 sanadiyyar ayyukan ta’addanci mabambanta a shekarar, amma guda 1,245 kacal aka shigar a rubuce a shekarar 2019.”
A jumullance,mace mace sanadiyyar ta’addanci a duniya ya ragu da kaso 15.5% daga shekarar 2018 zuwa 2019.

“Mace mace daga ta’addanci a Najeriya yanzu haka ya kai kaso 83%, ƙasa da adadin shekarar 2014 wanda shine mafi yawa da aka samu a tarihin ƙasar, sun ƙara da cewa har yanzu Najeriya na cikin haɗari sakamakon sabunta ayyukan a ta’addanci da ƙungiyar Boko Haram ta yi a ƙasar da maƙwabtanta irinsu Nijar,Kamaru,da Chadi,wanda yin hakan ya zamewa yankin babbar barazana.

“A shekarar 2019, Boko Haram ta aiwatar da hare-haren ƙunar baƙin wake guda 11 wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane 68, hare haren ƙunar baƙin wake suna da kaso 6% cikin mace mace sanadiyyar ayyukan ta’addancin Boko haram a shekarar 2019.

Labarai Makamanta