A yayin da Najeriya ke shirin bikin cika shekaru 60 da samun ‘yancin kai, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana Najeriya a matsayin kasar bakar fata da suka fi kowa samun cigaba a duniya da kuma tattalin arziki.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Femi Adesina, ya fitar, shugaban kasar yana cewa: “A yau mun zagaya akan abubuwa na tarihi, inda muka fara gabatar da bukukuwa na murnar cikar Najeriya shekara 60.
“Murnar cika shekaru 60 da samun ‘yancin kai na da muhimmanci, amma cutar COVID-19, wacce ta addabi kowacce kasa ta duniya ta sanya komai ya canja, hakan ya sanya muka gabatar da bikin ba kamar yadda aka saba gabatarwa ba.
“Najeriya kasa dake da yawan mutane sama da miliyan 200, da suke da tsantsar basira, muna da matukar muhimmanci a idon duniya”.
Wannan a gare ni wani abun alfahari ne. Duk inda ka shiga a duniya, ‘yan Najeriya ne kan gaba, ko a bangaren ilimi, bangaren kasuwanci, bangaren cigaba, bangaren nishadi, bangaren al’ada da sauransu.
“Haka kuma hoton gwal dake jikin taswirar mu na nuna cewa muna da matukar muhimmanci, ‘yan Najeriya na da matukar muhimmanci a idon duniya”.
Duka wadannan abubuwa sune suka saka muka zama kasar da tafi kowacce kasar bakar fata cigaba a duniya, sannan kuma ta zama kasar da tafi kowacce karfin tattalin arziki a Afrika.
“Wannan babban abin alfahari ne ga mutanen da suke aiki sau da kafa domin cigaban kasar.”