Ministan harkokin noma da cigaban karkara, Muhammad Sabo Nanono ya bayyana cewa akwai abubuwan da za su sa kasar ta yi murna da zuwan rana irin ta yau, 1 ga watan Oktoba, wato ranar bikin ‘yancin kai duk da irin kalubalen da ake fuskanta a Najeriya, nasarorin da aka samu a Najeriya sun cancanci ayi murna.
“Ina yi maku murna ‘yan Najeriya na cika shekaru 60 da samun ‘yanci a kasarmu. Murnar samun ‘yancin-kai abu ne da ya kamata ayi farin-ciki.”
Ministan harkar noman ya kara da cewa dole ayi la’akari da nasarorin da aka samu duk da tulin kalubale da ƙasar ke fama da su.“
A shekarar 2019, Najeriya ta kasance kasar da ta fi kowace kasa noman shinkafa a Nahiyar Afrika, ta doke kasar Masar a karon farko a tarihi.” Inji Sabo Nanono.
Ministan ya kara da cewa: “Wadannan nasarorin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne na farfaɗo da sha’anin noma.”
“Mu na bukatar hadin-kai tsakanin gwamnati da manoma domin a inganta kokarinmu. Najeriya ta na da karfin da za ta ciyar da kasar nan da makwabta.”
Jawabin ministan ya fito ne a shafinsa na Tuwita, @NanonoSabo, a ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoba, 2020.