Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabi a ranar da Najeriya ke cika shekara 62 da samun ?ancin kai.
Wannan ne jawabin Shugaba Buhari na ?arshe a irin wannan rana ta samun ?ancin kai a matsayinsa na shugaban ?asar Najeriya ganin cewa zai sauka a 2023.
Cikin abubuwan da ya yi magana a kai a yayin jawabin har da batun gudanar da sahihin za?e a 2023.
Ga dai wasu daga cikin abubuwan da shugaban ya yi magana a kan su:
Ha?aka t?attalin arziki, ya?i da cin hanci da inganta tsaro
C?ikin abubuwan da Shugaba Buhari ya yi magana a kansu a yayin jawabin da ya yi har da batun ha?aka tattalin arizikin Najeriya inda ya ce tun a lokacin da aka za?e shi, ya yi al?awarin ha?aka tattalin arzi?i, ya?i da cin hanci da rashawa da kuma inganta tsaro.
S?hugaban ya bayyana cewa da?in da?awa kan wa?annan al?awuran, gwamnatinsa ta kuma sha alwashi da yin tsayuwar daka wajen ganin cewa ta cire ?an Najeriya miliyan 100 daga cikin talauci a cikin shekara goma.
S?ai dai shugaban ya bayyana cewa da taimakon Ubangiji, gwamnatinsa ta yi matu?ar ?o?ari wurin cika wa?annan al?awuran da goyon bayan ?an ?asar da dama amma duk da haka a cewarsa kwaliyya ba ta kammala biyan ku?in sabulu ba.
S?hugaban ya bayyana cewa ?aya daga cikin wuraren da gwamnatinsa ta yi matu?ar ?o?ari shi ne bangaren ya?i da cin hanci inda ya ce sakamakon inganta ?angarorin ya?i da cin hanci da kuma taimakon ?asashen waje an mayar da ku?aden haram masu yawa da aka sace aka fitar waje.
Ta ?angaren tsaro kuma, shugaban ya bayyana cewa an yi ?o?ari wajen rage rikicin da ake yi a arewa maso gabashin ?asar, da rikicin ?an tayar da ?ayar baya a yankin Neja Delta da kuma rikice-rikicen ?abilanci a wasu sassa na Najeriya da sauran matsalolin da ke yi wa ?asar barazana.
H?aka kuma Shugaba Buhari ya yaba wa gwamnatinsa sakamakon tsare-tsaren da ta yi amfani da su wurin fita daga matsin tattalin arzikin da ta shiga har sau biyu.
I?nganta harkar noma
A? yayin jawabin nasa, Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ta bai wa ?angaren noma fifiko ta hanyar fito da ?anana da matsakaitan shirye-shirye da suka samar da ayyuka ga miliyoyin mutane.
S?hugaban ya kawo misali da shirye-shirye irin su Anchor Borrower wanda ya ce ?an Najeriya sun samu tagomashi ta bangaren samun wadataccen abinci da kuma jawo hankalinsu kan ?aukar noma a matsayin sana’a.
S?hugaban ya bayyana cewa fitar da kayayyaki da ?asar ke yi musamman amfanin gona da sauran abubuwa na kimiyya da fasaha za su taimaka wa kasuwar hada-hadar ku?i ta ?asar.
Y?ajin aikin ASUU
S?hugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a yayin jawabin nasa ya bayyana cewa yana matu?ar ba?in ciki sakamakon cikas da ake samu akai-akai a ?angaren ilimin gaba da sakandare a ?asar.
“Ina kira ga ?ungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU da ta koma aji kuma ina ba su tabbacin cewa zan share musu hawayensu da ?an abin da muke da shi duk da muna rashin ku?i,” in ji shi.
S?hugaban ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta yi ?o?ari wurin magance matsalar wadda aka shafe shekara 11 ana fama da ita.
S?hugaba Buhari ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta yi ?o?ari wurin tattara ku?i a ciki da wajen ?asar domin tallafa wa ?angaren ilimi don tabbatar da cewa ?an ?asar sun samu ingantaccen ilimi.
G?udanar da sahihin za?e a 2023
Kan batun za?e kuwa, Shugaba Buhari ya yi al?awarin ?ara inganta harkar za?e a ?asar a yayin da ake fuskantar za?en 2023 da ke tafe.
S?hugaban ya bayyana cewa duk wani ci gaba da aka samu a ?asar idan ba a za?i shugabanni ta ingantacciyar hanya ba duk wani ?o?ari da aka yi ba zai isa ba.
S?hugaban ya kawo misali da za?en da aka yi a kwanakin baya a Jihohin Anambra da Ekiti da Osun da wasu maza?un tarayya inda ya ce an yi za?en gaskiya da gaskiya.
G?ame da za?en 2023 da ke tafe, shugaban ya yi kira ga ?an takara da su gudanar da ya?in neman zabensu cikin lumana da kuma kiyayewa daga kalaman ?atanci ga juna.
H?aka kuma shugaban ya bayyana cewa yana sa ran za a samu ?arin matasa da mata a za?en da za a gudanar da ke tafe.
K?iwon lafiya
S?hugaba Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi ?o?ari matu?a wurin inganta ?angaren kiwon lafiya.
Y?a bayyana cewa musamman idan aka yi duba da lokacin annobar korona, ?asar ta taka rawar gani da har ya sa ?asashen duniya suka jinjina mata.
S?hugaban ya bayyana cewa Najeriya na daga cikin ?asashen duniya da ta ba mara ?a kunya ta hanyar juriya da mayar da hankali bayan duniya ta yi hashen cewa tana daga cikin ?asashen da annobar korona za ta yi wa ?arna