Naira 234 Ya Kamata A Sayar Da Litar Mai Ba 162 Ba – NNPC

Shugaban kamfanin mai na ?asa, NNPC, Mele Kyari ya ce gwamnatin tarayya na biyan naira biliyan 120 a kowanne wata a matsayin tallafin man fetur.

Kyari ya fadi hakan ne a taro na musamman da ministoci ke yi wa maneman labarai bayani karo na biyar da aka gudanar a fadar gwamnatin Najeriya a Abuja.

An ruwaito cewa Kyari ya ce, a maimakon ‘?an ?asar su dinga sayen mai kan yadda farashin ku?a?en shigo da adana shi suke na naira 234 kan kowace lita guda, gwamnati na sayar da man a kan naira 162, don haka ita ke ?aukan nauyin cikon ku?in.

Sai dai ya ?ara da cewa, NNPC ba zai iya ci gaba da asarar wa?anan ku?a?e ba, don hakan ‘?an Najeriya nan bada jimawa ba za su koma sayen man yada aka samo shi.

Ya kuma shaida cewa dole ne a bar kasuwa ta ?ayyade yada farashin mai zai kasance a ?asar.

Related posts

Leave a Comment