NAFDAC Ta Gargadi Masu Bleaching

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa NAFDAC, ta gargadi ‘yan kasar da su ƙaurace wa amfani da kayan kwalliyar da kan sauya fatar jikin bil adama daga baƙa zuwa fara.

Ta bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Olusayo Akintola ya aike wa manema labarai ranar Lahadi.

NAFDAC ta umarci a kama da gurfanar da wadanda suke tallata wannan sinadari ba tare da sahalewar hukumomin kasar ba.

Ta ce an haramta wadannan kayayyaki, saboda suna da lahani ga fata da wasu sassan bil adama kamar hanta da koda.

Labarai Makamanta

Leave a Reply