Na Yi Tir Da Kakaba Tikitin Musulmi Da Musulmi A Kaduna – Walid Jibrin

An bayyana matakin da wasu ‘yan siyasa ke ɗauka na yin amfani da addini domin cimma wata manufa ta son zuciyarsa a matsayin abin da bai dace ba kuma abin Allah wadai ne.

Tsohon shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP Sanata Walid Jibrin ne ya bayyana hakan, a yayin wani taron manema labarai da ya kira a Kaduna.

Walid Jibrin ya bada misali da kalaman tsohon Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El Rufai da yake tinkaho da cewar ya yi nasarar ƙaƙaba tikitin musulmi da Musulmi a jihar da cewar abin takaici ne.
“Najeriya kasa ce mallakin musulmi da kirista kuma kowanne yana da ‘yanci na gudanar da addinin shi bisa ga haka ba ƙaramin kuskure bane wani ya yi yunkurin tsame wasu a sha’anin gudanar da mulki.

Sanata Walid Jibrin ya koka dangane da yadda yake fuskantar hare haren ta’addanci daga wasu da bai tantance ba, inda yace sau biyu ana kai mishi hari a gidan da yake haya a Abuja da nufin ganin bayansa.

Jibrin ya ce harin baya bayan nan da aka kai mishi maharan sun zo cikin manyan motocin alfarma kirar Jip guda bakwai a gidan da yake haya a yankin APO Abuja da zimmar neman kudi har naira biliyan biyar.

“Ina amfani da wannan dama in sanar da dukkanin jama’a ba ni da wadannan kudi da ake tunani, hasali ma gidan da nake a Abuja haya nake yi, sannan ba ni da gidan kaina a Abuja ko babban birnin jihar da na fito Lafiya jihar Nasarawa, ballantana ajiye wadannan makudan kudade.

Labarai Makamanta

Leave a Reply